Dataset Viewer
Auto-converted to Parquet Duplicate
text
stringlengths
739
15.6k
Asalin hoton, Getty Images Donald Trump, shugaban da ya sake komawa Fadar Gwamnatin Amurka (White House ) a watan Janairu da alƙawarin zama mai wanzar da zaman lafiya, abin mamaki ya jefa ƙasarsa cikin yaƙin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila. Saɓanin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan da ya sak...
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/06/2025. Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed Aƙalla mutum bakwai ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani harin da Rasha ta kai da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa a daren j...
Asalin hoton, @ubasanius Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta tabbatar da bin haƙƙin mutanen jiharta matafiya da aka kashe a jihar Filato a ranar Asabar. Mutum 12 aka kashe ƴan asalin jihar Kaduna a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato yayin da suke kan hanyar zuwa ɗaurin auren ɗan'uwa...
Asalin hoton, Stocktrek / Getty Images Musayar wuta da ake yi tsakanin Isra'ila da Iran ta jawo fargabar yiwuwar Iran ta datse hada-hadar jiragen ruwa a mashigar Hurmuz, wanda shi ne hanyar dakon man fetur mafi muhimmanci a duniya. Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai...
Asalin hoton, Getty Images Arsenal na tunanin janye tayin fam miliyan 70 da ta gabatar kan ɗan wasan RB Leipzig Benjamin Sesko, mai shekara 22, sakamakon albashin da ɗan wasan na Slovenia ke buƙata, yayin da za ta iya karkata akalarta zuwa kan ɗan wasan Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27. (Mirror) Manch...
Asalin hoton, Alexander Denisenko Iran ta sake yin barazanar ficewa daga yarjejeniyar taƙaita yaɗuwar makaman nukiliya, yayin da ake tsaka da yaƙi tsakaninta da Isra'ila. A ranar 13 ga watan Yuni ne Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin soji da ƙwararrun masana nukiliyar Iran da wsu wuraren da ake zargi na d...
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/06/2025 Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin, nan muka kawo ƙarshen labaran da muke kawo muku na kai-tsaye a wannan rana ta Lahadi. Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya nuna mana. A madad...
Asalin hoton, EPA Da Benjamin Netanyahu ya fito domin jawabi game da halin da ake ciki a game da yaƙin da suke yi da Iran a ofishinsa na firaminista a safiyar yau, an riga an samu labarin harin Amurka da ya kawo sauyi dangane da yaƙin. Ya yi jawabin ne da Ingilishi, inda ya fito ƙarara ya yaba wa Amurka da shugabanta D...
A makon da ya gabata ne wasu ƙasashen Afirka uku suka gabatar tare da amince da kasafin kuɗinsu na shekarar da muke ciki, a wani mataki na bunƙasa tatattalin arzikin ƙasashen. Ƙasashen Kenya da Tanzaniya da kuma Uganda sun gabatar da kasafin kuɗin da ya mayar hankali kan zaɓuka da tattalin arzikin ƙasashen. A kowace s...
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku dukkan abubuwan dake wakana a fannin wasanni a faɗin duniya daga Asabar 21 zuwa Juma'a 28 ga watan Yunin 2025 Mohammed Abdu Asalin hoton, Getty Images Kociyan River Plate, Marcelo Gallardo yana da tabbacin za su iya doke Inter Milan a wasa na uku a rukuni na biyar a Club World Cup, d...
Asalin hoton, PA Media Golan Manchester United Andre Onana, mai shekara 29, yana son ya ci gaba da zama a filin wasan Old Trafford duk da cewa Monaco na zawarcin ɗan wasan na Kamaru. (Guardian) Zakarun Italiya Napoli sun bi sahun Inter Milan wajen zawarcin ɗan wasan gaban Manchester United Rasmus Hojlund, mai shekara 2...
Asalin hoton, Getty Images Juventus a Serie A na sha'awar ɗanwasan Manchester United Jadon Sancho a wannan bazara yayin da zakarun Italiya - Napoli ke cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗanwasan Ingilan mai shekara 25 wanda ya shafe kakar da ta gabata yana matsayin aro a Chelsea. (Sky Sports, external) Zarin Liverpool na ...
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labarai na wasanni a faɗin duniya daga 15 zuwa 21 ga watan Yunin 2025. Umar Mikail Asalin hoton, Getty Images Ɗan wasan bayan Ingila, Myles Lewis-Skelly ya amince da tsawaita zamansa a Arsenal. Matashin mai shekara 18 ya amince da tsawaita zamansa a Gunners na zuwa nan da wasu s...
Asalin hoton, Getty Images Chelsea na shirin yi wa Newcastle karen tsaye wajen ɗaukan ɗanwasan Brighton da Brazil Joao Pedro mai shekara 23. (Sun) Ɗanwasan Chelsea da Ingila Noni Madueke mai shekara 23 na haskawa a wajen ƙungiyoyi da dama a wannan bazara har da Arsenal. (Telegraph - subscription needed) Har yanzu Liver...
Asalin hoton, Presidency Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi. Tun farkon makon ne aka batun tazarcen shugaba Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima a matsayin mataimaki, lamarin da ya fara jefa jam'iyyar APC cikin ruɗani bayan abin da ya f...
Asalin hoton, @ZagazOlaMakama Ƙaruwar hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya na ƙara jefa fargaba kan makomar yankin inda masana tsaro suka ce akwai buƙatar sauya salon yaƙi. Wannan na zuwa bayan wani mummunan harin ƙunar bakin wake da aka kai a garin Konduga a jihar Borno a ranar Juma'a da ya kashe mutan...
Asalin hoton, Getty Images Duk da cewa an daɗe ana kallon mata a matsayin masu rauni idan aka kwatanta su da maza, wasu bincike da aka yi suna nuna akwai abubuwa da matan suka fi maza. Mata sun fi maza juriya wajen gudanar da aikace-aikace da dama a tare da isar da saƙo sama da maza. Sannan sun fi haƙuri da juriya. Bay...
Asalin hoton, AFP Rahotanni daga garin Tozai a karamar hukumar Isa da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya na cewa baki-ɗayan al'ummar garin sun tsere zuwa jihohi makwafta saboda hare-haren 'ƴan bindiga da suka addabi yankin. Rahotannin sun bayyana cewa a ƴan kwanakin da suka gabata, ƴan bindigar sun halaka m...
Asalin hoton, Boko Haram Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da harin da wata ƴar ƙunar bakin wake ta kai a babbar kasuwar kifi da ke Konduga, inda ta ce aƙalla mutum 10 sun mutu, duk da wata majiya ta ce aƙalla mutum 20 ne suka mutu, ciki har da ƴan sa-kai da suke taimakon sojoji wajen yaƙin da ƴan ƙungiyar. A daren ...
Ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata Asalin hoton, NESE ARI/ ANADOLU / GETTY IMAGES Asalin hoton, Per-Anders Pettersson / Getty Images Asalin hoton, SIYABONGA SOKHELA / GALLO IMAGES / GETTY IMAGES Asalin hoton, PAT BATARD / HANS LUCAS / AFP / GETTY IMAGES Asalin hoto...
Asalin hoton, Getty Images Isra'il da Iran na ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu, yayin da Donald Trump ya ce sai nan da mako biyu ne zai yanke shawarar yiwuwar shigar Amurka cikin yakin ko akasin haka. Ƙwararru a BBC da wakilanta sun masa wasu muhimman tambayoyi kan yaƙin daga masu bibiyarmu da masu yi a shafin inta...
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/06/2025 Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye. Sai kuma gobe Asabar idan Allah ya nuna mana. A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake c...
Asalin hoton, AFP Da alama wasu 'yan Najeriya sun zaburo domin magance wa kansu matsalar ƴan bindiga da ta addabi yankunansu. Al'ummar wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato sun yi haɗin gwiwa da sojoji inda suke kai wa ƴan bindiga hari har maɓoyarsu, a maimakon su jira ƴan bindigar su kawo masu hari s...
Asalin hoton, Getty Images Idan aka tambayi matasa da dama a Najeriya – musamman a Arewacin ƙasar – mece ce Dalar Gyaɗa? Da wuya ka samu wanda zai iya ba da amsa mai gamsarwa. Amma a da, kafin a gano man fetur a Najeriya, noma da fitar da gyaɗa na daga cikin manyan hanyoyin da ƙasar ke samun kuɗin shiga. Wannan ne ya ...
Asalin hoton, Corbis via Getty Images A ranar Juma'a 13 ga watan Yuni ne, Isra'ila ta bayyana cewa ta ƙaddamar da hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran da na sojin ƙasar, da nufin ruguza shirin nukiliyarta da ƙarfin sojinta, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu. Hare-haren na zuwa ne bayan da Hukumar...
Asalin hoton, EPA Yayin da yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran ya shiga mako guda, dakarun rundunar juyin juya hali ta IRGC na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare da yin amfani da samfuran makamai iri-iri. Gidan talbijin na Iran ya ce sun kai hari kan tashar ruwan Isra'ila a Haifa da cibiyar tattara bayanan sirri ta Isra'ila d...
Asalin hoton, Reuters A halin yanzu rikicin da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran ya takaita ne ga kasashen biyu. Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe na ta kira kan cewa a yi taka-tsantsan. To amma me zai faru idan kasashen biyu suka ki jin shawarar yin taka-tsantsan? Haka nan me zai faru idan yakin ya bazu kuma ...
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/06/2025. Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida Asalin hoton, Getty Images Shugaba Trump ya ce sai nan da mako biyu zai yanke hukunci kan ko zai shigar wa Isra'ila yaƙin da take yi da Iran ko kuma akasin haka. A wata sanarwa da ...
Hikayata gasa ce ta rubutun ƙagaggun gajerun labarai ta mata zalla wadda ke samar da dama ga mata zalla marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa. Dole ne labaran da za a shiga su kasance ƙagaggun labarai kan wani jigo. Mata biyu na iya haɗa gw...
Asalin hoton, Getty Images Kafafen yaɗa labaru a Afirka sun wallafa martani mabambanta daga ƙasashen Afirka tun bayan ɓarkewar yaki tsakanin Isra'ila da Iran. Kuma bayanan da suka fito daga gwamnatocin ƙasashen ya nuna yadda batun tattalin arziƙi da na diflomasiyya da kuma aƙida suka shafi matsayar da suka ɗauka. Ƙasas...
Asalin hoton, AFP Mayakan kungiyar nan ta Lakurawa sun gargadi al'ummomin garuruwa fiye da goma na yankin karamar hukumar Augie ta jihar Kebbi, a kan su yi watsi da dabarar sayar da shanun huda suna sayen wasu na'urorin zamani na huda da ke amfani da man fetur. Mayakan sun ce za su halaka duk wanda ya ki jin gargadin n...
Asalin hoton, ARAFA SALIM SAID Cutar sikila ko amosanin jini na ɗaya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS. Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da i...
Asalin hoton, US Air Force Daga cikin makaman da za a iya harbawa su keta ƙarƙashin ƙasa har su iso wurin da rumbunan ajiyar sinadaran nukiliyar Iran suke, daya ne kawai ba a yi amfani da shi ba zuwa yanzu, kuma Isra'ila ba ta da shi a yanzu. Makamin shi ne GBU-57A/B - wanda ya kasance bom marar nukiliya mafi ƙarfi a d...
Matsalolin kiwon lafiya da suka haɗa da fashewar mahaifa na daga cikin manyan dalilan da ke sanya wa a juyar da mahaifar mace. A cewar likitoci ana yi wa mace aiki ne a asibiti idan za a juyar da mahaifarta. Haka kuma ba a yin tiyatar sai da yardarta da na miji ko makusantanta. Matar da aka yi wa juyen mahaifa bata sa...
Sashen Hausa na BBC yana watsa shirye-shirye guda huɗu a kowace rana, na tsawon minti talatin-talatin cikin harshen Hausa. Akwai shirin Safe, akwai shirin Hantsi, akwai shirin Rana, sannan kuma akwai shirin Dare, dukkaninsu a lokutta kamar haka. A gajeren zango. Lokutan su ne: 0530,0630,1400,1930 GMT. Ga masu saurare a...

Dataset Card for "bbc-hausa"

More Information needed

Downloads last month
10