image imagewidth (px) 336 707 | transcript stringlengths 12 39 |
|---|---|
Waƙar Infiraji Ta Farko | |
Waƙar Majidu | |
Bismi l-Lāh al-Raḥmān al-Raḥīm | |
Wa ṣalla l-Lāhu ʿalā l-Nabiyyi l-Karīmi | |
Wa ʿalā ālihī wa ṣaḥbih wa sallam | |
Bismil l-Lāhi Majīdi | |
Na yi nufin waƙa jadīdī | |
In yabon manzo ḥamīdī | |
Dhu shafā Yawmal Miʿādi | |
Mai sonsa ba zai baƙin ciki ba | |
Rabbanā ya daɗin aminci | |
Gun mafificin mutunci | |
Ɗa wani nasa ɗan karumci | |
Wanda ka ba shugabanci | |
Ya yi horo ba da kangara ba | |
Rabbi na nufi wagga waƙa | |
Ta yabo nasa ba nifāqā | |
Taimake ni ka ban ḥadhāqā | |
In yi waƙa mai zalāqā | |
Ta yabo nasa ba da kuskure ba | |
Rabbanā ka yi min ijābā | |
In ga nai sallah a Ɗaiba | |
Har in tada ido in duba | |
In ga Koran nan ta gubba | |
In yi murna ba da fariya ba | |
Ya Ilāha l-ʿālamina | |
Taimakan ni in je Madina | |
In ji daɗi in yi murna | |
In ga qabrin ɗan Amina | |
Baban Kulthumu ɗan Suwaiba | |
A dare ka yi min ishārā | |
In ga na je nai ziyara | |
Gun kushewan na da nura | |
Ta cika shi na mai bushara | |
Ga Musulmi ba da kangara ba | |
Ka ji mai waƙar hululu | |
Tūba zanka yabon Rasulu | |
Musɗafa jikankKhalīlu | |
Gobe ka sha salsabīlu | |
Wanda ya fi ruwan zuma a gumba | |
Don mutum ne shi karimi | |
Mai yawan haƙuri ḥalīmi | |
Ya abokina ʿAsīmi | |
In ka so ka zame salami | |
Ya bi Annabi ba da sunkuye ba | |
Kafirai da sun fahimta | |
Bin Muhammadu ya kamata | |
Ambato nasa ya gabata | |
Can ga Attaura, ku huta | |
Ku bi Annabi ba da gardama ba | |
Ya kamata mu gode Allah | |
Can gabanmu akwai qabīla | |
An kashe su cikin jahālā | |
Mu zuwansa tazan fitilla | |
A gare mu ba mu yi zaman duhu ba | |
Shekarar ƙarnin dashensa | |
Ya katarta da maʼu nisa | |
Shi muke cin arzikinsa | |
Ka ga ba don shi ba da sa- | |
Muwa ba ta riski mai rashi ba | |
A’a in ba ka mayyaze ba | |
Gaskiya ba ta sa fita ba | |
Sai da ya zaka nuna turba | |
Ko duhu bai wartsake ba | |
Ba dan aiko shi duniya ba | |
Ɗan Amina muna yabonka | |
Don mafificin rabonka | |
Nai duʿaāʿi in gane ka | |
Zuciyata ba ta harka | |
In ban yi yabonka na natsa ba | |
Sanda an aiko shi shirya | |
Gaskiya ta kori ƙarya | |
Masu aikin ratse hanya | |
Ƙi da so wasu sun biyayya | |
Tamkar ba su gaji kangara ba | |
Shi mutum ne mai laɗafa | |
Kyan jiki da hali da siffa | |
Na ga Annabi ba khilāfā | |
Ko a baiwa ya fi sarfa | |
Ba shi kan kyauta shina bari ba | |
Ba shi rowa don ƙiyayya | |
An yi sammu gami da cinya | |
Aka ba shi a kan hamayya | |
Don yawan ladabi da kunya | |
Ya ci ba bisa kan rashin sani ba | |
Hankalinsa yana ga Allah | |
Bai kula ba, maras kasala | |
Gun yawan azumi da salla | |
Taimakonsa yana ga Allah | |
Ya ko isa jalla bai gaza ba | |
Rabbanā ya baza wanjin | |
Masu ƙinsa sabo da ƙwanjin | |
Arzikinsa ya haske ƙirjin | |
Annabinsa aboka bar jin | |
Maganarsu ba su yi muwāfaqā ba | |
Shi ya ɗaukaka ɓirbishinsu | |
Hassadarsu ta hallaka su | |
Aka karkashe galibinsu | |
Galibin wasu masu mussu | |
Suka tuba da sake ba shi gaba |
No dataset card yet
- Downloads last month
- 170