0
stringlengths
3
620
1
stringlengths
4
423
So Noah, his wife, and his sons and their wives left the boat.
Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa,
And all of the large and small animals and birds came out of the boat, pair by pair.
da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu.
Then Noah built an altar to the Lord , and there he sacrificed as burnt offerings the animals and birds that had been approved for that purpose.
Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji , ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden.
And the Lord was pleased with the aroma of the sacrifice and said to himself, “I will never again curse the ground because of the human race, even though everything they think or imagine is bent toward evil from childhood. I will never again destroy all living things.
Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.
As long as the earth remains, there will be planting and harvest, cold and heat, summer and winter, day and night.”
“Muddin duniya tana nan, lokacin shuki da na girbi, lokacin sanyi da na zafi, lokacin damina da na rani, dare da rana ba za su daina ba.”
Then God blessed Noah and his sons and told them, “Be fruitful and multiply. Fill the earth.
Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya.
All the animals of the earth, all the birds of the sky, all the small animals that scurry along the ground, and all the fish in the sea will look on you with fear and terror. I have placed them in your power.
Dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifayen teku, za su riƙa jin tsoronku, suna fargaba. An sa su a cikin hannuwanku.
I have given them to you for food, just as I have given you grain and vegetables.
Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.
But you must never eat any meat that still has the lifeblood in it.
“Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna.
“And I will require the blood of anyone who takes another person’s life. If a wild animal kills a person, it must die. And anyone who murders a fellow human must die.
Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.
If anyone takes a human life, that person’s life will also be taken by human hands. For God made human beings in his own image.
“Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum.
Now be fruitful and multiply, and repopulate the earth.”
Amma ku, ku yi ta haihuwa, ku ƙaru; ku yaɗu a duniya, ku yi yawa a bisanta.”
Then God told Noah and his sons,
Sai Allah ya ce wa Nuhu da ’ya’yansa,
“I hereby confirm my covenant with you and your descendants,
“Yanzu na kafa alkawarina da ku da zuriyarku a bayanku,
and with all the animals that were on the boat with you—the birds, the livestock, and all the wild animals—every living creature on earth.
da kowace halitta mai rai wadda ta kasance tare da kai; wato, tsuntsaye da dabbobin gida da kuma dukan namun jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin; wato, kowane mai rai na duniya.
Yes, I am confirming my covenant with you. Never again will floodwaters kill all living creatures; never again will a flood destroy the earth.”
Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba.”
Then God said, “I am giving you a sign of my covenant with you and with all living creatures, for all generations to come.
Allah ya kuma ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na yi tsakanina da ku, da kowace halitta tare da ku; alkawari na dukan zamanai masu zuwa.
I have placed my rainbow in the clouds. It is the sign of my covenant with you and with all the earth.
Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya.
When I send clouds over the earth, the rainbow will appear in the clouds,
Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan,
and I will remember my covenant with you and with all living creatures. Never again will the floodwaters destroy all life.
zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba.
When I see the rainbow in the clouds, I will remember the eternal covenant between God and every living creature on earth.”
Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.”
Then God said to Noah, “Yes, this rainbow is the sign of the covenant I am confirming with all the creatures on earth.”
Saboda haka Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na kafa tsakanina da dukan masu rai a duniya.”
The sons of Noah who came out of the boat with their father were Shem, Ham, and Japheth. (Ham is the father of Canaan.)
’Ya’yan Nuhu maza, waɗanda suka fito daga cikin jirgi, su ne, Shem, Ham da Yafet. (Ham shi ne mahaifin Kan’ana.)
From these three sons of Noah came all the people who now populate the earth.
Waɗannan su ne ’ya’yan Nuhu maza uku, daga gare su ne kuma duniya za tă cika da mutane.
After the flood, Noah began to cultivate the ground, and he planted a vineyard.
Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi.
One day he drank some wine he had made, and he became drunk and lay naked inside his tent.
Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa.
Ham, the father of Canaan, saw that his father was naked and went outside and told his brothers.
Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje.
Then Shem and Japheth took a robe, held it over their shoulders, and backed into the tent to cover their father. As they did this, they looked the other way so they would not see him naked.
Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu.
When Noah woke up from his stupor, he learned what Ham, his youngest son, had done.
Sa’ad da Nuhu ya farka daga buguwarsa ya kuma gane abin da ƙarami ɗansa ya yi,
Then he cursed Canaan, the son of Ham: “May Canaan be cursed! May he be the lowest of servants to his relatives.”
sai ya ce, “Kan’ana la’ananne ne, zai zama bawa mafi ƙanƙanta ga ’yan’uwansa.”
Then Noah said, “May the Lord , the God of Shem, be blessed, and may Canaan be his servant!
Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem.
May God expand the territory of Japheth! May Japheth share the prosperity of Shem, and may Canaan be his servant.”
Allah yă ƙara fāɗin ƙasar Yafet; bari Yafet yă zauna a tentunan Shem, bari kuma Kan’ana yă zama bawansa.”
Noah lived another 350 years after the great flood.
Bayan ambaliyar, Nuhu ya yi shekaru 350.
He lived 950 years, and then he died.
Gaba ɗaya dai, Nuhu ya yi shekara 950, sa’an nan ya mutu.
This is the account of the families of Shem, Ham, and Japheth, the three sons of Noah. Many children were born to them after the great flood.
Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
The descendants of Japheth were Gomer, Magog, Madai, Javan, Tubal, Meshech, and Tiras.
’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
The descendants of Gomer were Ashkenaz, Riphath, and Togarmah.
’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
The descendants of Javan were Elishah, Tarshish, Kittim, and Rodanim.
’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
Their descendants became the seafaring peoples that spread out to various lands, each identified by its own language, clan, and national identity.
(Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
The descendants of Ham were Cush, Mizraim, Put, and Canaan.
’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
The descendants of Cush were Seba, Havilah, Sabtah, Raamah, and Sabteca. The descendants of Raamah were Sheba and Dedan.
’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan.
Cush was also the ancestor of Nimrod, who was the first heroic warrior on earth.
Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya.
Since he was the greatest hunter in the world, his name became proverbial. People would say, “This man is like Nimrod, the greatest hunter in the world.”
Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji . Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji .
He built his kingdom in the land of Babylonia, with the cities of Babylon, Erech, Akkad, and Calneh.
Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
From there he expanded his territory to Assyria, building the cities of Nineveh, Rehoboth-ir, Calah,
Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala
and Resen (the great city located between Nineveh and Calah).
da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
Mizraim was the ancestor of the Ludites, Anamites, Lehabites, Naphtuhites,
Mizrayim shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa,
Pathrusites, Casluhites, and the Caphtorites, from whom the Philistines came.
Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
Canaan’s oldest son was Sidon, the ancestor of the Sidonians. Canaan was also the ancestor of the Hittites,
Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,
Jebusites, Amorites, Girgashites,
Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa,
Hivites, Arkites, Sinites,
Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
Arvadites, Zemarites, and Hamathites. The Canaanite clans eventually spread out,
Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu
and the territory of Canaan extended from Sidon in the north to Gerar and Gaza in the south, and east as far as Sodom, Gomorrah, Admah, and Zeboiim, near Lasha.
har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
These were the descendants of Ham, identified by clan, language, territory, and national identity.
Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
Sons were also born to Shem, the older brother of Japheth. Shem was the ancestor of all the descendants of Eber.
Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
The descendants of Shem were Elam, Asshur, Arphaxad, Lud, and Aram.
’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
The descendants of Aram were Uz, Hul, Gether, and Mash.
’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash.
Arphaxad was the father of Shelah, and Shelah was the father of Eber.
Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
Eber had two sons. The first was named Peleg (which means “division”), for during his lifetime the people of the world were divided into different language groups. His brother’s name was Joktan.
Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.
Joktan was the ancestor of Almodad, Sheleph, Hazarmaveth, Jerah,
Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,
Hadoram, Uzal, Diklah,
Hadoram, Uzal, Dikla,
Obal, Abimael, Sheba,
Obal, Abimayel, Sheba,
Ophir, Havilah, and Jobab. All these were descendants of Joktan.
Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
The territory they occupied extended from Mesha all the way to Sephar in the eastern mountains.
Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
These were the descendants of Shem, identified by clan, language, territory, and national identity.
Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
These are the clans that descended from Noah’s sons, arranged by nation according to their lines of descent. All the nations of the earth descended from these clans after the great flood.
Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.
At one time all the people of the world spoke the same language and used the same words.
To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.
As the people migrated to the east, they found a plain in the land of Babylonia and settled there.
Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.
They began saying to each other, “Let’s make bricks and harden them with fire.” (In this region bricks were used instead of stone, and tar was used for mortar.)
Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.
Then they said, “Come, let’s build a great city for ourselves with a tower that reaches into the sky. This will make us famous and keep us from being scattered all over the world.”
Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”
But the Lord came down to look at the city and the tower the people were building.
Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.
“Look!” he said. “The people are united, and they all speak the same language. After this, nothing they set out to do will be impossible for them!
Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.
Come, let’s go down and confuse the people with different languages. Then they won’t be able to understand each other.”
Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”
In that way, the Lord scattered them all over the world, and they stopped building the city.
Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin.
That is why the city was called Babel, because that is where the Lord confused the people with different languages. In this way he scattered them all over the world.
Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.
This is the account of Shem’s family. Two years after the great flood, when Shem was 100 years old, he became the father of Arphaxad.
Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad.
After the birth of Arphaxad, Shem lived another 500 years and had other sons and daughters.
Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
When Arphaxad was 35 years old, he became the father of Shelah.
Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela.
After the birth of Shelah, Arphaxad lived another 403 years and had other sons and daughters.
Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
When Shelah was 30 years old, he became the father of Eber.
Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber.
After the birth of Eber, Shelah lived another 403 years and had other sons and daughters.
Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
When Eber was 34 years old, he became the father of Peleg.
Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg.
After the birth of Peleg, Eber lived another 430 years and had other sons and daughters.
Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
When Peleg was 30 years old, he became the father of Reu.
Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu.
After the birth of Reu, Peleg lived another 209 years and had other sons and daughters.
Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
When Reu was 32 years old, he became the father of Serug.
Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug.
After the birth of Serug, Reu lived another 207 years and had other sons and daughters.
Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
When Serug was 30 years old, he became the father of Nahor.
Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor.
After the birth of Nahor, Serug lived another 200 years and had other sons and daughters.
Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
When Nahor was 29 years old, he became the father of Terah.
Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera.
After the birth of Terah, Nahor lived another 119 years and had other sons and daughters.
Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata.
After Terah was 70 years old, he became the father of Abram, Nahor, and Haran.
Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.
This is the account of Terah’s family. Terah was the father of Abram, Nahor, and Haran; and Haran was the father of Lot.
Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.
But Haran died in Ur of the Chaldeans, the land of his birth, while his father, Terah, was still living.
Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa.
Meanwhile, Abram and Nahor both married. The name of Abram’s wife was Sarai, and the name of Nahor’s wife was Milcah. (Milcah and her sister Iscah were daughters of Nahor’s brother Haran.)
Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita ’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska.
But Sarai was unable to become pregnant and had no children.
Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.
One day Terah took his son Abram, his daughter-in-law Sarai (his son Abram’s wife), and his grandson Lot (his son Haran’s child) and moved away from Ur of the Chaldeans. He was headed for the land of Canaan, but they stopped at Haran and settled there.
Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.
Terah lived for 205 years and died while still in Haran.
Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.
The Lord had said to Abram, “Leave your native country, your relatives, and your father’s family, and go to the land that I will show you.
Ubangiji ya ce wa Abram, “Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.
I will make you into a great nation. I will bless you and make you famous, and you will be a blessing to others.
“Zan mai da kai al’umma mai girma, zan kuma albarkace ka; zan sa sunanka yă zama mai girma, ka kuma zama sanadin albarka.