id
stringlengths
1
5
url
stringlengths
31
212
title
stringlengths
1
128
text
stringlengths
100
4.26k
13738
https://ha.wikipedia.org/wiki/Aderonke%20Adeniyi%20Esther
Aderonke Adeniyi Esther
Aderonke Adeniyi aka Sikemi (an haife tane a 15 ga watan Nuwamba) yar'Najeriya ce yar fim kuma mai shirya fina-finan a kamfanin yin fim na Nollywood. Takasance ne anfi saninta da shirye-shiryenta da take yi acikin harshen Yorubanci fina-finai. Farkon rayuwa An haife tane a ranar 15 ga watan Nuwamba a jihar Oyo Najeriya 蓷a ta biyu a cikin iyali shida. Ta halarci makarantar Kinder Land Nursery da Primary school,a jihar Oyo; Kwalejin Polytechnic ne na Ibadan a Jihar Oyo inda ta samo mata takardar shaidar difloma ta kasa sannan kuma Mui Authentic School of Drama domin yin karatun digirin tana biyu. Aiki Ta sami digirin tane a fannin yin zane-zane ne daga wata makaranta mai suna Authentic School of Drama kuma ta shiga masana'antar sosai a 2007. sannan Tayi fice a karon farko a fim din Ebure na 2007. A shekara ta 2014, ta fitar da fim din ta na farko, Sikemi Ta ci gaba da samar da Iboju a shekara ta 2015, Ajaga da Aya Wa a shekara ta 2016 da sabon fitowar ta, Twisted a 2018. Ta kuma yi fice a farnin fina-finai da yawa kamar, Iku Ewa, Oyenusi, Atori, Ogede Dudu, Orisirisi, Iranran da sauran su. Rayuwarta Aderonke Adeniyi, mahaifiya ce mara miji ga ya'yanta yara biyu Kyautuka da girmamawa Mainland TV Show Show da lambar yabo mafi kyawun Actress (2017) Kyautar Green View Nishadi Nollywood Namijin Namiji (Na mace) (2018) Fina-finai Ebure (2008) Iku Ewa (2009) Oyenusi (2009) Jemiriye (2011) Ogede Dudu (2009) Sikemi (2014) Aljanna ta wauta (2015) Atori (2015) Iboju (2015) Woto (2016) Ajaga (2016) Orisirisi (2016) Iranran (2016) Aya Wa (2017) Twisted (2018) Duba kuma Jerin 'yan fim din Najeriya Manazarta Haifaffun
30367
https://ha.wikipedia.org/wiki/Nana%20Oye%20Lithur
Nana Oye Lithur
Nana Oye Lithur yar Ghana ce kuma barista kuma 'yar siyasa. Ta kasance ministar kula da jinsi, yara da kare zamantakewa a Ghana daga shekara ta, 2013 zuwa 2017, wanda shugaba John Mahama ya nada bayan babban zaben Ghana. Ita mamba ce ta National Democratic Congress. Tarihin rayuwa Ta yi karatu a Makarantar Cocin Ridge da Wesley Girls' High School. Ta sami digiri na farko a fannin shari'a a Jami'ar Ghana, Legon, da kuma digiri na biyu a fannin shari'a, 'yancin 蓷an adam da dimokra蓷iyya a Afirka daga Jami'ar Pretoria, Afirka ta Kudu. Ta rike mukaman babban darektan cibiyar kare hakkin bil adama da kuma mai kula da yankin (Ofishin Afirka) na kungiyar kare hakkin dan adam ta Commonwealth. Ta yi aiki a matsayin memba na kwamitin gudanarwa na 茦ungiyar 茦asa ta Duniya akan Zubar da ciki da kuma mamba mai ba da shawara na 茦ungiyar 茦asa ta Duniya kan Gane Ha茩茩in Haihuwa. Kyaututtuka da karramawa Wanda ta kar蓳i lambar yabo ta Jagorancin Bawan Afirka na (2011) Kyautar Gwarzon Ha茩茩in Mata na (2012) Matan Afirka ta Yamma a Kyautar Jagoranci don Tasiri Mai Girma Manazarta Rayayyun