uhura / ha_mc1_train.json
ebayes's picture
Upload 30 files
597042a verified
raw
history blame
73.1 kB
[
{
"question": "Alamomin (:) da (-) ana kiran su",
"a": "ruwa biyu da karan ɗori",
"b": "saɓi-zarce da aya",
"c": "baka biyu da alamar tambaya",
"d": "alamar motsin rai da waƙafi",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "Idan bauna ta hudo ta baya da sanda, me zai faru?",
"a": "Bude baki[Maryam Sa21]",
"b": "Kawo sura.",
"c": "Fada",
"d": "Tafiya lafiya",
"answerKey": "a",
"context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18] maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "‘‘Shi ke sa ƙasa ta koma baya, Cikin duniya da lalaci’’\nWane abu mawaƙin nan yake nufi a wannan baiti daga Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja?",
"a": "Jahilci",
"b": "Shashanci",
"c": "Hassada",
"d": "Giba",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Song"
},
{
"question": "Ga garinku na nufin ...",
"a": "mutu",
"b": "firgita",
"c": "ba da gari",
"d": "mai da gari",
"answerKey": "a",
"context": "A kwanakin Sarkin Katsina Jan-Hazo, Kwararrafawa suka je Katsina. Sarkinsu ya sauka yammacin gari a babbar ruga, wazirinsa kuma a gabashin gari. Sarkin ya kama mashinsa ya girgiza shi ya jefa cikin gari, ya fada tsohuwar kasuwa kusa da kududdufin Taukin Daule, sai wuta ta kama gun. Daga nan sarakunan Katsina suka taru wajen Sarki Jan-Hazo, suka yi kus- kus haka suka gamu a kan su fita su bar garin, mai tsira ya tsira, mai mutuwa ya mutu. Sai suka aika wa Malam Danmasani. Shi kuwa ya ce kada su fita, za su ga abin da Allah zai yi da Kwararrafawa. Ya dukufa rokon Ubangiji bisa wannan lamari.\n \nSai Sarkin Kwararrafawa ya tashi don ya duba dokinsa, amma dokin ya shure shi a kan cibiya da dare ya fadi matacce. Da aka ba wazirinsa labarin abin da ya faru, sai nan da nan shi ma ya hau dokinsa, dokin ya ka da shi wuyansa ya karye, ya mutu. A cikin daren nan kuma manya-manyan sarakunansu bakwai suka ce ga garinku. Sai niyyar Kwararrafawa ta yaki ta wargaje, suka bar wajen. Daga nan Sarkin Katsina da kansa ya tafi wajen Danmasani ya durkusa ya yi masa godiya tare da goma na arziki.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Wane abu ne bauna take yi wa wanda yake biye\nda ita?",
"a": "Saurin bacewa da yankan baya.",
"b": "Tsayawa wuri guda.",
"c": "Layar kare da tserewa.",
"d": "Zagayawa da sauri.",
"answerKey": "a",
"context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18] maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Shahon[Maryam Sa27] farauta akan dauke shi a",
"a": "kafada.",
"b": "wuya.",
"c": "ka.",
"d": "hannu.",
"answerKey": "a",
"context": "Tsuntsaye wadanda ke farautar nama suna da halitta daidai wadda za ta dace da wannan aiki. Ga baki mai[Maryam Sa25] karfi da kaifi ya lankwasa kamar kugiya. Da shi suke kekketa nama. Ga su da kafa mai karfi da kumba zako-zako. In sun kawo sura, da su su ke fyauce[Maryam Sa26] abin da suka farauta, su rike, su yi sama da shi. In za su ci, sai su kakkafa kumbobinsu ciki, su rike shi kam.\n Shaho yana da saurin tafiya. Akwai wasu iri, in sun ga wani tsuntsu yana tashi sai su bi, kome saurin tashinsa, sai sun ishe sun buge. Su irin wadannan, mutane sun dade suna kiwon su domin farauta. In za a farauta, sai ka dauki shahonka a kafada, an daure shi da sarka, an yi masa lullubi. In ka ga ko hasbiya tana tashi, sai ka bude kan shahonka ka sake shi, ya buge\nmaka.\nWannan irin farauta ta shahara a kasashen su Farisa da Hindu. Da, hara Turai an yi, amma yanzu an daina.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Su wane ne suka ƙago rubutun abacada?\n",
"a": "Fonisiyawa",
"b": "Larabawa",
"c": "Romawa",
"d": "Turawa",
"answerKey": "a",
"context": "Karanta wannan labari a natse, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye da shi.\n \nMutanen Fonisiya, ƙasar nan ta bakin teku kusa da Siiya su ne suka fara ƙago rubutun abacada kimanin shekaru 3,400 da suka wuce. Wato su suna amfani da baƙaƙe da wasula 22 ne wajen rubutunsu. Sai Romawa suka ɗauki samfurin rubutun Fonisiyawa bayan kimanin shekaru 1,000, suka tsara rubuta harshensu na Latin ta yin amfani da bakaken abacada 23. Turawa kuma su suka koyi salon yin amfani da abacada irin na Latin. Irin wannan rubutu na Latin wanda ake yin\namfani da shi wajen rubuta harshen Turanci shi ne a Hausa alke kira rubutun boko.\n A fasalin rubutu mai amfani da baƙaƙe da wasula kuma, sai rubutun Larabci wanda shi ma yake amfani da wadansu alamnomi masu wakiltar muryoyi ko saututtuka irin na abacada, amma waɗanda suke da fasali daban da irin na rubutun Latin (wato boko), domin shi rubutun Larabci ana fara yin sa ne daga dama ana tafiya hagu, kuna ana kyasta wasulla a kan baƙaƙen ne, maimakon jeranta baƙi da wasali da ake yi a rubun boko. Shi dai rubutun Larabci ana jin an fara amfani da shi ne kimanin shekaru 2000 da suka wuce.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "ldan har wanda bauna ta biyo ya haye itace Iange-lange, to me za ta yi masa?",
"a": "Sai ta kai karo ya karye.",
"b": "Sai ta yi la susa.",
"c": "Sai ta yi lasa.",
"d": "Sai ta yi ta kallo.",
"answerKey": "a",
"context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18] maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Fitar Kutsu na nufin .",
"a": "wadda babu shiri",
"b": "maras amfani",
"c": "wadda aika yi da daddare",
"d": "wadda aka yi da sassafe",
"answerKey": "a",
"context": "A shekara ta 1897 zamanin Sarkin Bida Abubakar, Turawa suka yi karon batta da Nufawa. Kafin nan, Turawa sun shekara uku cur suna godo da sarki su hadu da shi cikin aminci a wani wuri da ake kira Egbaji, yana kin zuwa. Har ma a wani lokaci sai da Turawan suka nada wani Muhammadu Makun a madadinsa. Duk da haka a cikin 1900 kusan a ce sarki biyu ke akwai a Bida, tsohon sarki da wanda Turawa suka nada.\n Ana cikin haka, ran nan dai sai Gwamna Lugga ya aika wa Sarkin Bida da takarda, ya ce masa ya dai yi kokari ya zo ya sadu da shi a fadar Kogin Kaduna, kuma kada ya ii tsoron kome. Gwamna ya kara da cewa ba abin da za a yi masa, zai zo lafiya ya koma\nlafiya.\n A wannan karon ma sai Sarkin Bida ya ki zuwa. Makun ne da 'yan rakiyarsa suka amsa kira, suka je wurin Gwamna Lugga. Saboda haka Turawa suka dauri aniyar zuwa Bida. Suka shaida wa jama'a muddin dai ba an taba su ba, babu fada. Kuma duk mutumin da suka ga don ganin su ya yi haramar gudu, za su dauke shi a mazaunin makiyinsu. Har ma Gwamna Lugga ya aika wa Sarki Abubakar da cewa kodayake dai Makun ne suka dauka kamar sarki, duk da haka idan shi\nAbubakar ya yarda suka sadu ko a Bida ne, ba zai wulakanta shi ba. Zai sa shi cikin jin dadi har abada.\nAmma duk a banza. Maimnakon ya tauso sai ya gudu ya tasar wa Lafai. Amma fa fitar kutsu ya yi, domin daga shi sai fadawa kamar shida ya bar Bida Aka yi irin abin nan wuji-wuji-ina-gabas, aka i xashe[Maryam Sa8] manyan sarakunansa, aka yi wa wadansu iaur[Maryam Sa9] , aka kama na kamawa. Wadanda aka kama bayan sun wartsake sarai aka sake su. ",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Me bayi suka samu wajen Turawa?",
"a": "Daurin gindi",
"b": "Yabo",
"c": "Aikin yi",
"d": "matsi",
"answerKey": "a",
"context": "Bayan shekara biyu da lakwame Sakkwato sai al'amarin bauta ya yi sauki. Bayi suka sami damar kai kara dakin shari'a idan suna bukatar su fanshi kansu. Kuma idan har mutum yana da bawa, bawan nan ya nuna yana so a 'yanta shi, amma ubangijinsa ya kekasa Kasa, da cewa bawan nan ya garzaya ga sarkin Musulmi, sai sarki ya ce a kyale shi ya tafi abinsa. Wato mai shi ya yi raguwar dabara ke nan, domin da ya bari sun shirya tun a gida tilas ne kuma an yarda bawan nan ya fanshi kansa. Ma' ana, ya rika yin aiki yana samun kudi yana bai wa maigidansa har ya gama fansar kansa. Abin da ya sa maganar bautar nan ta fi karfi a Sakkwato a fili yake. Da farko dai an sha fadar yadda Sauran kasashe ke kai gaisuwar bayi can. Saboda haka babu inda bauta ta yi karfi kamar a Sakkwato. Turawa ka nuna wa jama'a a fili cewa duk wanda yake son 'yanci yana iya samun sa, wanda kuma ya zauna cikin kangin bauta shi ya so.\n Ba a dade da samun galaba kan Sakkwato ba sai aka fara maganar yadda za a jarraba koya wa almajirai karatun Turawa a can. Amma abin bai yi nasara ba. Jama'a suna gani kamar karatun Turawa wani sabon addini ne daban. Saboda haka sai aka yi watsi da lamarin.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "An tsara Kukan Kurciya na M. B. Bambale",
"a": "kashi-kashi da fitowa-fitowa",
"b": "fitowa-fitowa da shiga-shiga",
"c": "rabo-rabo da kashi-kashi",
"d": "shiga-shiga da rabo-rabo",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Theatre"
},
{
"question": "Wanne ne ɗan jirge?",
"a": "/l/",
"b": "/t/",
"c": "/m/",
"d": "/sh/",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "Mene ne jigon ‘Waƙar Hana Zalunci’ ta Salihu Kwantagora a Waƙoƙin Hausa?",
"a": "Saɓa wa tafarkin adalci",
"b": "Saɓa wa tafarkin lalaci",
"c": "Jahilci",
"d": "Fariya",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Song"
},
{
"question": "Kwata",
"a": "Mayankar dabbobi[Maryam Sa17]",
"b": "Kara",
"c": "Masayar dabbobi",
"d": "Maciya",
"answerKey": "a",
"context": "Kudan gida na daya daga cikin abokan gabarmu. manya masu raba cuta ga 'ya Adam. Shi ke kawo su, atuni', da ciwon gudawa da sauran irinsu.\n Amma shi kuda ba ya cizon mu kamar sauro da Isando. Hanyar da ya ke bi ya yi nasa mugun aiki ba daya ba ce da tasu. Su, suna tsotso kwayoyin cuta daga Cikin jini ne, su je su soki mai lafiya su dura masa. Amma bakin kuda ba a yi shi don ya yi cizo ba. Kuda ba ya iya huda fatar mutum, ba ya ma iya huda fatar kome, ko yana so. Harshensa da bakinsa duka taushi\ngare su.\nTsaya ka ji kazantar kuda. Ka san lalle, ko ba don cuta ba, kuda abin kyama ne. Wajibi ne kuma mu yi iyakar kokarinmu mu rabu da shi.\nBa abin da kuda ke so kamar ya ci luroson (najasar) dan Adam. In ya samu najasa, ya duka da ci, sai ka ce ka samu taliya. Kun san kuwa, in mutum ba shi da lafiya sau da yawa akan sami kwayoyin cuta a cikin najarsa.\nKai duk dai wurin kazanta, Mahauta ne, juji ne, wurin mushe ne, wurin gyambo ne duka dai nan ne fadar kuda.\n In sun ci sun taso, sai su yi face-face da kazantar har da kwayoyin cutar da ke ciki.\nDa ma kafafuwansu da ikinsu gashi gare Su, duk kuwa madauka dauda ne.\n \nDaga nan sai su zo su sauka kan abincinmu. \nKan san galibi, abincinmu wanda suka fi so shi ne kilishi, tsire, nono, sukari da su alewa. Kaga wadannan, in an saya ba a sake dafa su. saboda haka muna cin kazanta da yawa daga gare su.\n Ban da wannan ma, in suna cin abincinmu, sukan rika amai bisansa suna tashi. Kazanta bisa kazanta! Ina ka ga lafiya?\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Sarkin Kwararralawa mutun ne mai…..",
"a": "sihiri",
"b": "son abin duniya",
"c": "Hakuri",
"d": "kwarjini",
"answerKey": "a",
"context": "A kwanakin Sarkin Katsina Jan-Hazo, Kwararrafawa suka je Katsina. Sarkinsu ya sauka yammacin gari a babbar ruga, wazirinsa kuma a gabashin gari. Sarkin ya kama mashinsa ya girgiza shi ya jefa cikin gari, ya fada tsohuwar kasuwa kusa da kududdufin Taukin Daule, sai wuta ta kama gun. Daga nan sarakunan Katsina suka taru wajen Sarki Jan-Hazo, suka yi kus- kus haka suka gamu a kan su fita su bar garin, mai tsira ya tsira, mai mutuwa ya mutu. Sai suka aika wa Malam Danmasani. Shi kuwa ya ce kada su fita, za su ga abin da Allah zai yi da Kwararrafawa. Ya dukufa rokon Ubangiji bisa wannan lamari.\n \nSai Sarkin Kwararrafawa ya tashi don ya duba dokinsa, amma dokin ya shure shi a kan cibiya da dare ya fadi matacce. Da aka ba wazirinsa labarin abin da ya faru, sai nan da nan shi ma ya hau dokinsa, dokin ya ka da shi wuyansa ya karye, ya mutu. A cikin daren nan kuma manya-manyan sarakunansu bakwai suka ce ga garinku. Sai niyyar Kwararrafawa ta yaki ta wargaje, suka bar wajen. Daga nan Sarkin Katsina da kansa ya tafi wajen Danmasani ya durkusa ya yi masa godiya tare da goma na arziki.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "‘‘Malam Jatau, ka san yarinyar nan da ke zaune a ƙusurwar ɗaki, ga ta can ta leƙo da kanta ta taga?’’\nWanda ya yi wannan magana a Jatau Na Kyallu na S. Maƙarfi, shi ne",
"a": "Alƙali",
"b": "Ɗanwanka",
"c": "Muhuti",
"d": "Jamanu",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Theatre"
},
{
"question": "Unguwanni, kalma ce mai gaɓoɓi",
"a": "huɗu",
"b": "shida",
"c": "biyar",
"d": "bakwai",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "Ina aka kai su Kasa bayan an yanke musu hukunci?",
"a": "Kurkuku.",
"b": "Yamma da Magumi.",
"c": "Ga shugaban makaranta.",
"d": "Tsauni.",
"answerKey": "a",
"context": "A wani gari can yamma da Magumi, wai shi Tsauni, an yi wani yaro mai suna Salihi. Iyayensa ba masu wadata ba ne, amma sun yi ƙoƙarin ganin ya yi ilmin boko da na Arabiya. Bayan Salihi ya kammala karatun firamare, sai mahaifinsa Tanimu, ya nema masa makarantar gaba da firamare. Domin an ce ‘‘Ilimi gishirin zaman duniya.’’ Amma kuma samo wa Salihi babbar makarantar Magumi bai yi wa mahaifiyarsa Ɗahira daɗi ba, don ba ta son ɗanta ya yi nesa da ita. Dalili shi ne ɗansu tilo namiji, sauran huɗun kuwa duk mata ne. Bugu da ƙari, tana jin munanan labarai iri-iri da kan faru a irin waɗannan makarantu.\n\nBayan Salihi ya isa makaranta, sai ya duƙufa kan karatu gadan-gadan. Zuwansa ke da wuya, sai suka ƙulla abota da wani ɗan ajinsu, wai shi Kasa. Kafin ya ankara, sai da abokinsa ya jefa shi cikin wata ƙungiyar asiri.\n\nDa ya farga da halin da ya shiga, sai ya yi ƙoƙarin fita daga cikinta, amma aka nuna masa ai ba a haka. ‘‘ In har ka ce za ka fice, lallai za a kassara ka, ko ma a halaka ka’’ in ji abokinsa.\n\nGanin halin tsaka-mai-wuya da ya shiga, sai ya tsayar da shawarar ya fallasa ƙungiyar, in ya so komai ta tafasa ta ƙone. Ya je ya shaida wa shugaban makaranta. Nan take ya sanya jami’an tsaro suka kamo dukkan ‘yan ƙungiyar. Kotu ta yanke musu hukunci, sannan aka kai su gidan jarun. Da ma an ce, ‘‘ Komai nisan jifa ƙasa za ya faɗo.’’",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Wanne ne gaskiya dangane da ƙissa?",
"a": "Tana da alaƙa da addini",
"b": "Yara ake yi wa don koyon tarbiyya",
"c": "Dole a samu Gizo da Ƙoƙi a cikinta",
"d": "Dole a samu aljanu a cikinta",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "Labarin ya na nuna cewa Bahaushe yakan yi noma domin",
"a": "guje wa yunwa",
"b": "wadatar zuci",
"c": "ƙarin aure",
"d": "neman kuɗi",
"answerKey": "a",
"context": "Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayuwarsu, domin duk wata fafitika da gwama numfashi da ba hammata iska, ana yi wa ciki ne. Wato cikin biyu: ɗaya ya yiwu an ci an ƙoshi, ko kuma ana cikin halin nema ne.\n\nKullum, da zaran gari ya waye, wasu tun da jijjifi, za a ga sun fita neman abin da za su ci, su da iyalansu, domin a samu rufin asiri. Saboda haka, ba a barin kowa a gida sai tsofaffi da mata da yara da kuma ragwage, kowa ya tafi neman halaliya.\n\nA al’adance, Hausawa suna da lokuta uku na cin abinci a kowace rana, wato safe da rana da dare. A mafi yawan lokuta da safe akan sha abu mai ruwa-ruwa, kamar koko da ƙosai ko kunu. Wasu kuma, sukan ɗumama abin da aka ci a daren da ya gabata. Da rana, kuma akan dafa duk irin abin da ya samu kamar shinkafa da wake ko dambu ko kuma ɗanwake. Da daddare kuma, kusan kowane gida za a sa mu cewa ana dafa tuwo da miya ne, ko miyar kuka ko kuɓewa ko taushe ko kalkashi da dai sauransu, da nama ko babu nama. Duk ko ma mene ne ya samu, wato dai “Daidai ruwa daidai ƙurji.”\n\nHar ila yau, ko da yake ba kowa yake da ƙarfin ɗora girki sau uku ba a rana saboda halin yau, amma a kan sami maƙwabta na gari masu tausayi da lura, su kan kira maƙwabtansu domin su ci abincin, ko suna da shi ko ba su da shi. Da ma tunfil-azal, an san Bahaushe da halin taimako ga ɗan’uwansa.\n\nA zamanin da, za a ga Bahaushe yana ƙoƙarin ya yi noma domin kada gidansa a zauna da yunwa. Amma yanzu, zamananci ya mayar da tunaninsa ya koma kan kasuwanci ko aikin ofis a maimakon aikin gona saboda lalaci da son jiki.",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "‘‘Mu tsere wa ci uku nana, ba Mu abincimmu babu ha’inci.’’\nA wannan baiti na waƙar ‘Mu Yaƙi Jahilci’ ta Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja, an yi amfani da",
"a": "saɓi - zarce",
"b": "alamci",
"c": "jerin sarƙe",
"d": "mutumtarwa",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Song"
},
{
"question": "Wase ba ta jin taɗin mutanen Yalwa domin…",
"a": "ba sa ga-maciji",
"b": "sun yi nisa da juna",
"c": "raba su da aka yi",
"d": "fashi da ake yawan yi",
"answerKey": "a",
"context": "“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe, ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Abin da ya mamaye labarin Shaihu Umar shi ne",
"a": "bauta da cinikin bayi",
"b": "noma da kiwo",
"c": "karatu da almajiranci",
"d": "farauta da noman rake",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Literature"
},
{
"question": "Wane irin amfanin gona Malam Nomau ya kai\nkasuwar Wudil?",
"a": "Hannu banza ya shiga kasuwar.",
"b": "Busasshiyar kubewa.",
"c": "Tumatur da tattasai.",
"d": "Sabuwar masara.",
"answerKey": "a",
"context": "Yau Jumma'a Malam Nomau za shi cin kasuwa Wudil. Kafin ya tafi ya dauki wandonsa mai kamun kafa, ya bude ya sa shi ya zuba babbar rigarsa bullan da hular dara da falmaran, da takalmi sani tsalle, da 'yar ciki, da rawani mubarashi ya rataye shi. Kuma yana saye da wando buje da 'yar shara, da hula habar kada da takalmin fade.\nDa isowarsa kofar gari sai ya raba gindin wata tsamiya ya fito da kayan nan nasa na cikin wando ya caba ado bayan ya wanke jikinsa. Ya kuma zuba turare dan-goma, ya bara goro marsa ya cika bakinsa ya yi kumurya. Ya kunshe tsofaffin kayansa buje, ya make a hammatarsa ya shiga gari ya kai gidan abokinsa ya ajiye. Matar abokinsa ta ba shi farau-farau ya sha. Daga nan sai ya tafi cin kasuwa.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "anya bante ga yara maza a al’adar Bahaushe, na faruwa ne daga",
"a": "lokacin da aka sha yaro ya warke",
"b": "lokacin da yaro ya fara tafiya",
"c": "shekara uku da haihuwa",
"d": "shekara biyu da haihuwa",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Wanne ne habaici daga cikin waɗannan?",
"a": "Ƙaton kai kamar tulu",
"b": "Kano tumbin giwa",
"c": "Tsame tsakin tsamiya daga tsakin tsada",
"d": "Da karo-karo giwa ta fi kowa",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "Wanne ne biki na sana’a?",
"a": "Bikin kamun kifi.",
"b": "Bikin kamun gwauro.",
"c": "Bikin saukar karatu.",
"d": "Bikin kalankuwa.",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Ziƙau a labarin na nufin",
"a": "babu kuɗi",
"b": "da mummunar kama",
"c": "babu mutunci",
"d": "a galabaice",
"answerKey": "a",
"context": "‘‘Ba neman aure ke da wuya ba, shigaka-fito’’. Ka ga shiga-ka-fito ɗin nan, lallai shiga-ka-fito ɗin ne! Domin aljihu kan jigata kafin a kai ga biki. Tuddan da al’ada ta tanada, waɗanda dole sai an haye su, suna da yawa.\n\nYanzu ɗauki misalin kayan na–gani-inaso, wato ’yan kayan nan da ake shiryawa a kai gidan su yarinya a karon farko. Ma’anar yin haka, wai iyaye su san cewa manemin auren ’yarsu da gaske yake. To, ina dole ga yin haka? Da can da yake zuwa yana zance da ’yarsu yana yi mata hasafi, ba a san da gaske yake ba?\n\nGangaro kan kayan toshi. Nan ma tsabagen kuɗi ake kashewa a sayi suturu da kayan shafe-shafe a kai wa yarinya. Kada fa ka ce zuwa zance da manemi yake yana yi wa yarinya kyauta mako-mako, shi ke nan, ya wadatar. Ina, ko kaɗan!\n\nKada ka mance da kuɗin gaisuwar iyaye da dukiyar aure kafin a yi baiko da sa ranar biki. Kuɗi ne maɗiɗɗiki ake tanada a kai wa iyayen yarinya da niyyar dai wannan abu da aka ambata.\n\nDuk bayan wannan, ana sa ranar aure, manemin yarinya ya dosa karakaina ke nan daga wannan gida zuwa wancan, ko ma wannan gari zuwa wancan da sunan gayar da iyaye da kakanninta, wai don su san shi. I, za su san shi mana, tun da ba yana zuwa ne ziƙau ba! Da zarar biki ya kawo jiki kuma, uwa-uba za a shirya kayan lefe na fitar hankali a kai wa yarinya. Nan ma dukiya ake narkawa.\n\nHaƙiƙa duk waɗannan abubuwa al’ada ce kawai ta ƙaƙaba wa al’umma. Ai ta fuskar dukiya, muhimmin abu ga aure, sadaki. Amma abin takaici, yanzu an yi masa mahalli a can ƙarshen sahu!",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Cikin waɗannan, wanne ne ake kaɗawa?",
"a": "Jauje",
"b": "Molo",
"c": "Kwabsa",
"d": "Garaya",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "An tsara rubutun wasannin Zaman Duniya Iyawa Ne na Y. Ladan",
"a": "kashi-kashi da shiga-shiga",
"b": "rabo-rabo da fitowa-fitowa",
"c": "kashi-kashi da fitowa-fitowa",
"d": "rabo-rabo da shiga-shiga",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Theatre"
},
{
"question": "Daga cikin waɗannan bukukuwa a wanne ne ake ɗauri?",
"a": "kalankuwa",
"b": "buɗar dawa",
"c": "Sallar gani",
"d": "Sallar idi",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Ware kayan da bai dace da rukunin kayayyakin\nnan ba.",
"a": "Gyauto",
"b": "Jamfa.",
"c": "Wando.",
"d": "Falmaran.",
"answerKey": "a",
"context": "Yau Jumma'a Malam Nomau za shi cin kasuwa Wudil. Kafin ya tafi ya dauki wandonsa mai kamun kafa, ya bude ya sa shi ya zuba babbar rigarsa bullan da hular dara da falmaran, da takalmi sani tsalle, da 'yar ciki, da rawani mubarashi ya rataye shi. Kuma yana saye da wando buje da 'yar shara, da hula habar kada da takalmin fade.\nDa isowarsa kofar gari sai ya raba gindin wata tsamiya ya fito da kayan nan nasa na cikin wando ya caba ado bayan ya wanke jikinsa. Ya kuma zuba turare dan-goma, ya bara goro marsa ya cika bakinsa ya yi kumurya. Ya kunshe tsofaffin kayansa buje, ya make a hammatarsa ya shiga gari ya kai gidan abokinsa ya ajiye. Matar abokinsa ta ba shi farau-farau ya sha. Daga nan sai ya tafi cin kasuwa.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Da ya hango su, ya ce ‘‘Da wa Allah ya haɗa mu?’’ Wannan na nufin da ya hango su, Sai ya",
"a": "bi su a guje",
"b": "gudu",
"c": "ɓoye",
"d": "ja ya tsaya",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "A labarin an nuna baya ga shan abu mai ruwa-ruwa da safe, wasu Hausawa kan",
"a": "yi ɗumame",
"b": "dafa shinkafa",
"c": "yi tuwo",
"d": "turara dambu",
"answerKey": "a",
"context": "Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayuwarsu, domin duk wata fafitika da gwama numfashi da ba hammata iska, ana yi wa ciki ne. Wato cikin biyu: ɗaya ya yiwu an ci an ƙoshi, ko kuma ana cikin halin nema ne.\n\nKullum, da zaran gari ya waye, wasu tun da jijjifi, za a ga sun fita neman abin da za su ci, su da iyalansu, domin a samu rufin asiri. Saboda haka, ba a barin kowa a gida sai tsofaffi da mata da yara da kuma ragwage, kowa ya tafi neman halaliya.\n\nA al’adance, Hausawa suna da lokuta uku na cin abinci a kowace rana, wato safe da rana da dare. A mafi yawan lokuta da safe akan sha abu mai ruwa-ruwa, kamar koko da ƙosai ko kunu. Wasu kuma, sukan ɗumama abin da aka ci a daren da ya gabata. Da rana, kuma akan dafa duk irin abin da ya samu kamar shinkafa da wake ko dambu ko kuma ɗanwake. Da daddare kuma, kusan kowane gida za a sa mu cewa ana dafa tuwo da miya ne, ko miyar kuka ko kuɓewa ko taushe ko kalkashi da dai sauransu, da nama ko babu nama. Duk ko ma mene ne ya samu, wato dai “Daidai ruwa daidai ƙurji.”\n\nHar ila yau, ko da yake ba kowa yake da ƙarfin ɗora girki sau uku ba a rana saboda halin yau, amma a kan sami maƙwabta na gari masu tausayi da lura, su kan kira maƙwabtansu domin su ci abincin, ko suna da shi ko ba su da shi. Da ma tunfil-azal, an san Bahaushe da halin taimako ga ɗan’uwansa.\n\nA zamanin da, za a ga Bahaushe yana ƙoƙarin ya yi noma domin kada gidansa a zauna da yunwa. Amma yanzu, zamananci ya mayar da tunaninsa ya koma kan kasuwanci ko aikin ofis a maimakon aikin gona saboda lalaci da son jiki.",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Yadda ake samun tatsuniya a bakunan tsofaffi, haka ake samun ƙissa a bakunan malaman",
"a": "tarihi",
"b": "tsibbu",
"c": "fiƙihu",
"d": "hisabi",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": " Idan kuda ya sami turoson dan adam da ci. kai\nka ce mutum ya sami",
"a": "naman kaji:",
"b": "tuwon shinkafa.",
"c": "wake da shinkafa.",
"d": "shinkafa.",
"answerKey": "a",
"context": "Kudan gida na daya daga cikin abokan gabarmu. manya masu raba cuta ga 'ya Adam. Shi ke kawo su, atuni', da ciwon gudawa da sauran irinsu.\n Amma shi kuda ba ya cizon mu kamar sauro da Isando. Hanyar da ya ke bi ya yi nasa mugun aiki ba daya ba ce da tasu. Su, suna tsotso kwayoyin cuta daga Cikin jini ne, su je su soki mai lafiya su dura masa. Amma bakin kuda ba a yi shi don ya yi cizo ba. Kuda ba ya iya huda fatar mutum, ba ya ma iya huda fatar kome, ko yana so. Harshensa da bakinsa duka taushi\ngare su.\nTsaya ka ji kazantar kuda. Ka san lalle, ko ba don cuta ba, kuda abin kyama ne. Wajibi ne kuma mu yi iyakar kokarinmu mu rabu da shi.\nBa abin da kuda ke so kamar ya ci luroson (najasar) dan Adam. In ya samu najasa, ya duka da ci, sai ka ce ka samu taliya. Kun san kuwa, in mutum ba shi da lafiya sau da yawa akan sami kwayoyin cuta a cikin najarsa.\nKai duk dai wurin kazanta, Mahauta ne, juji ne, wurin mushe ne, wurin gyambo ne duka dai nan ne fadar kuda.\n In sun ci sun taso, sai su yi face-face da kazantar har da kwayoyin cutar da ke ciki.\nDa ma kafafuwansu da ikinsu gashi gare Su, duk kuwa madauka dauda ne.\n \nDaga nan sai su zo su sauka kan abincinmu. \nKan san galibi, abincinmu wanda suka fi so shi ne kilishi, tsire, nono, sukari da su alewa. Kaga wadannan, in an saya ba a sake dafa su. saboda haka muna cin kazanta da yawa daga gare su.\n Ban da wannan ma, in suna cin abincinmu, sukan rika amai bisansa suna tashi. Kazanta bisa kazanta! Ina ka ga lafiya?\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "‘‘Na haƙa ta ƙi haƙo, na rufe ta ƙi rufo.’’",
"a": "Inuwa",
"b": "Rana",
"c": "Marmaea",
"d": "Wata",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "Ɗan matar da ke aure a gidan da ba a nan ta haife shi ba, shi ne",
"a": "agola",
"b": "mowa",
"c": "bora",
"d": "kado",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Rabo nawa wasan Shaihu Umar na U. Ladan da D. Lyndersay ya ƙunsa?",
"a": "Biyu",
"b": "Uku",
"c": "Huɗu",
"d": "Biyar",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Theatre"
},
{
"question": "Lakwame[Maryam Sa6] na nufin ...",
"a": "kama",
"b": "bari",
"c": "gano",
"d": "farmaki",
"answerKey": "a",
"context": "Bayan shekara biyu da lakwame Sakkwato sai al'amarin bauta ya yi sauki. Bayi suka sami damar kai kara dakin shari'a idan suna bukatar su fanshi kansu. Kuma idan har mutum yana da bawa, bawan nan ya nuna yana so a 'yanta shi, amma ubangijinsa ya kekasa Kasa, da cewa bawan nan ya garzaya ga sarkin Musulmi, sai sarki ya ce a kyale shi ya tafi abinsa. Wato mai shi ya yi raguwar dabara ke nan, domin da ya bari sun shirya tun a gida tilas ne kuma an yarda bawan nan ya fanshi kansa. Ma' ana, ya rika yin aiki yana samun kudi yana bai wa maigidansa har ya gama fansar kansa. Abin da ya sa maganar bautar nan ta fi karfi a Sakkwato a fili yake. Da farko dai an sha fadar yadda Sauran kasashe ke kai gaisuwar bayi can. Saboda haka babu inda bauta ta yi karfi kamar a Sakkwato. Turawa ka nuna wa jama'a a fili cewa duk wanda yake son 'yanci yana iya samun sa, wanda kuma ya zauna cikin kangin bauta shi ya so.\n Ba a dade da samun galaba kan Sakkwato ba sai aka fara maganar yadda za a jarraba koya wa almajirai karatun Turawa a can. Amma abin bai yi nasara ba. Jama'a suna gani kamar karatun Turawa wani sabon addini ne daban. Saboda haka sai aka yi watsi da lamarin.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Da farko, wane abu ne dabbobi suka fi so su yi in har sun yi kicibis da mutum?",
"a": "gudu.",
"b": "magana.",
"c": "kauracewa.",
"d": "tsiya.",
"answerKey": "a",
"context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18] maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Maƙasudin ‘Waƙar ’Yan Baka’ ta Sa’adu Zungur shi ne",
"a": "daƙile jita-jita",
"b": "hana zunɗe",
"c": "daƙile almubazzaranci",
"d": "hana hassada",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Song"
},
{
"question": "Me ya kawo lafawar bauta?\n",
"a": "Cin sakkwato",
"b": "Yawan bayi.",
"c": "Sakacin Sakkwato.",
"d": "tawayen.",
"answerKey": "a",
"context": "Bayan shekara biyu da lakwame Sakkwato sai al'amarin bauta ya yi sauki. Bayi suka sami damar kai kara dakin shari'a idan suna bukatar su fanshi kansu. Kuma idan har mutum yana da bawa, bawan nan ya nuna yana so a 'yanta shi, amma ubangijinsa ya kekasa Kasa, da cewa bawan nan ya garzaya ga sarkin Musulmi, sai sarki ya ce a kyale shi ya tafi abinsa. Wato mai shi ya yi raguwar dabara ke nan, domin da ya bari sun shirya tun a gida tilas ne kuma an yarda bawan nan ya fanshi kansa. Ma' ana, ya rika yin aiki yana samun kudi yana bai wa maigidansa har ya gama fansar kansa. Abin da ya sa maganar bautar nan ta fi karfi a Sakkwato a fili yake. Da farko dai an sha fadar yadda Sauran kasashe ke kai gaisuwar bayi can. Saboda haka babu inda bauta ta yi karfi kamar a Sakkwato. Turawa ka nuna wa jama'a a fili cewa duk wanda yake son 'yanci yana iya samun sa, wanda kuma ya zauna cikin kangin bauta shi ya so.\n Ba a dade da samun galaba kan Sakkwato ba sai aka fara maganar yadda za a jarraba koya wa almajirai karatun Turawa a can. Amma abin bai yi nasara ba. Jama'a suna gani kamar karatun Turawa wani sabon addini ne daban. Saboda haka sai aka yi watsi da lamarin.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Jigon labarin ‘‘Kowa Ya Daka Rawar Wani’’ na Magana Jari Ce na III na A. na Imam, ya yi daidai da ‘‘kowa ya",
"a": "Tsaya Matsayinsa",
"b": "Ji a Jikinsa",
"c": "Ji da Kansa",
"d": "Shiga Taitayinsa",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Literature"
},
{
"question": "Wajibi",
"a": "Dole",
"b": "Abin so",
"c": "Haka ne",
"d": "Sunna",
"answerKey": "a",
"context": "Kudan gida na daya daga cikin abokan gabarmu. manya masu raba cuta ga 'ya Adam. Shi ke kawo su, atuni', da ciwon gudawa da sauran irinsu.\n Amma shi kuda ba ya cizon mu kamar sauro da Isando. Hanyar da ya ke bi ya yi nasa mugun aiki ba daya ba ce da tasu. Su, suna tsotso kwayoyin cuta daga Cikin jini ne, su je su soki mai lafiya su dura masa. Amma bakin kuda ba a yi shi don ya yi cizo ba. Kuda ba ya iya huda fatar mutum, ba ya ma iya huda fatar kome, ko yana so. Harshensa da bakinsa duka taushi\ngare su.\nTsaya ka ji kazantar kuda. Ka san lalle, ko ba don cuta ba, kuda abin kyama ne. Wajibi ne kuma mu yi iyakar kokarinmu mu rabu da shi.\nBa abin da kuda ke so kamar ya ci luroson (najasar) dan Adam. In ya samu najasa, ya duka da ci, sai ka ce ka samu taliya. Kun san kuwa, in mutum ba shi da lafiya sau da yawa akan sami kwayoyin cuta a cikin najarsa.\nKai duk dai wurin kazanta, Mahauta ne, juji ne, wurin mushe ne, wurin gyambo ne duka dai nan ne fadar kuda.\n In sun ci sun taso, sai su yi face-face da kazantar har da kwayoyin cutar da ke ciki.\nDa ma kafafuwansu da ikinsu gashi gare Su, duk kuwa madauka dauda ne.\n \nDaga nan sai su zo su sauka kan abincinmu. \nKan san galibi, abincinmu wanda suka fi so shi ne kilishi, tsire, nono, sukari da su alewa. Kaga wadannan, in an saya ba a sake dafa su. saboda haka muna cin kazanta da yawa daga gare su.\n Ban da wannan ma, in suna cin abincinmu, sukan rika amai bisansa suna tashi. Kazanta bisa kazanta! Ina ka ga lafiya?\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Marubucin ‘Waƙar Zambon ƙazama’ ta zaɓaɓɓun Waƙoƙin Da Da Na Yanzu na D. Abdulkadir ya nuna cewa mata ƙazamai suna nuna ƙazantarsu ta",
"a": "jiki gida da abinci",
"b": "gida da abinci",
"c": "jiki da abinci",
"d": "jiki gida da waje",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Song"
},
{
"question": "Yaya aka yi da fursunonin yaki?",
"a": "An sake su.",
"b": "An azabtar da su.",
"c": "An bautar da su.",
"d": "An kore su.",
"answerKey": "a",
"context": "A shekara ta 1897 zamanin Sarkin Bida Abubakar, Turawa suka yi karon batta da Nufawa. Kafin nan, Turawa sun shekara uku cur suna godo da sarki su hadu da shi cikin aminci a wani wuri da ake kira Egbaji, yana kin zuwa. Har ma a wani lokaci sai da Turawan suka nada wani Muhammadu Makun a madadinsa. Duk da haka a cikin 1900 kusan a ce sarki biyu ke akwai a Bida, tsohon sarki da wanda Turawa suka nada.\n Ana cikin haka, ran nan dai sai Gwamna Lugga ya aika wa Sarkin Bida da takarda, ya ce masa ya dai yi kokari ya zo ya sadu da shi a fadar Kogin Kaduna, kuma kada ya ii tsoron kome. Gwamna ya kara da cewa ba abin da za a yi masa, zai zo lafiya ya koma\nlafiya.\n A wannan karon ma sai Sarkin Bida ya ki zuwa. Makun ne da 'yan rakiyarsa suka amsa kira, suka je wurin Gwamna Lugga. Saboda haka Turawa suka dauri aniyar zuwa Bida. Suka shaida wa jama'a muddin dai ba an taba su ba, babu fada. Kuma duk mutumin da suka ga don ganin su ya yi haramar gudu, za su dauke shi a mazaunin makiyinsu. Har ma Gwamna Lugga ya aika wa Sarki Abubakar da cewa kodayake dai Makun ne suka dauka kamar sarki, duk da haka idan shi\nAbubakar ya yarda suka sadu ko a Bida ne, ba zai wulakanta shi ba. Zai sa shi cikin jin dadi har abada.\nAmma duk a banza. Maimnakon ya tauso sai ya gudu ya tasar wa Lafai. Amma fa fitar kutsu ya yi, domin daga shi sai fadawa kamar shida ya bar Bida Aka yi irin abin nan wuji-wuji-ina-gabas, aka i xashe[Maryam Sa8] manyan sarakunansa, aka yi wa wadansu iaur[Maryam Sa9] , aka kama na kamawa. Wadanda aka kama bayan sun wartsake sarai aka sake su. ",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Labarun cikin Magana Jari ce na III na A. Imam, an shirya su ne bisa salon",
"a": "ji ka ƙaru",
"b": "karɓa – karɓa",
"c": "koyi da kanka",
"d": "zaɓi da kanka",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Literature"
},
{
"question": "Kwana nawa mace ke yi a lokacin takaba?",
"a": "Ɗari da talatin",
"b": "Ɗari da arba’in",
"c": "Ɗari da hamsin",
"d": "Ɗari da sittin",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Wane take ya fi dacewa da wannan labari?",
"a": "‘Ramin ƙarya ƙurarre ne.’",
"b": "‘Ilimi gishirin zaman duniya.’",
"c": "‘Alheri danƙo ne …’",
"d": "‘Ba a fafar gora …’",
"answerKey": "a",
"context": "A wani gari can yamma da Magumi, wai shi Tsauni, an yi wani yaro mai suna Salihi. Iyayensa ba masu wadata ba ne, amma sun yi ƙoƙarin ganin ya yi ilmin boko da na Arabiya. Bayan Salihi ya kammala karatun firamare, sai mahaifinsa Tanimu, ya nema masa makarantar gaba da firamare. Domin an ce ‘‘Ilimi gishirin zaman duniya.’’ Amma kuma samo wa Salihi babbar makarantar Magumi bai yi wa mahaifiyarsa Ɗahira daɗi ba, don ba ta son ɗanta ya yi nesa da ita. Dalili shi ne ɗansu tilo namiji, sauran huɗun kuwa duk mata ne. Bugu da ƙari, tana jin munanan labarai iri-iri da kan faru a irin waɗannan makarantu.\n\nBayan Salihi ya isa makaranta, sai ya duƙufa kan karatu gadan-gadan. Zuwansa ke da wuya, sai suka ƙulla abota da wani ɗan ajinsu, wai shi Kasa. Kafin ya ankara, sai da abokinsa ya jefa shi cikin wata ƙungiyar asiri.\n\nDa ya farga da halin da ya shiga, sai ya yi ƙoƙarin fita daga cikinta, amma aka nuna masa ai ba a haka. ‘‘ In har ka ce za ka fice, lallai za a kassara ka, ko ma a halaka ka’’ in ji abokinsa.\n\nGanin halin tsaka-mai-wuya da ya shiga, sai ya tsayar da shawarar ya fallasa ƙungiyar, in ya so komai ta tafasa ta ƙone. Ya je ya shaida wa shugaban makaranta. Nan take ya sanya jami’an tsaro suka kamo dukkan ‘yan ƙungiyar. Kotu ta yanke musu hukunci, sannan aka kai su gidan jarun. Da ma an ce, ‘‘ Komai nisan jifa ƙasa za ya faɗo.’’",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Me ya faru ga wurin da mashin nan ya fadi?",
"a": "Wuta ta tashi.",
"b": "Hazo ya tashi.",
"c": "Wuta ta lafa.",
"d": "Wuta ta gagara.",
"answerKey": "a",
"context": "A kwanakin Sarkin Katsina Jan-Hazo, Kwararrafawa suka je Katsina. Sarkinsu ya sauka yammacin gari a babbar ruga, wazirinsa kuma a gabashin gari. Sarkin ya kama mashinsa ya girgiza shi ya jefa cikin gari, ya fada tsohuwar kasuwa kusa da kududdufin Taukin Daule, sai wuta ta kama gun. Daga nan sarakunan Katsina suka taru wajen Sarki Jan-Hazo, suka yi kus- kus haka suka gamu a kan su fita su bar garin, mai tsira ya tsira, mai mutuwa ya mutu. Sai suka aika wa Malam Danmasani. Shi kuwa ya ce kada su fita, za su ga abin da Allah zai yi da Kwararrafawa. Ya dukufa rokon Ubangiji bisa wannan lamari.\n \nSai Sarkin Kwararrafawa ya tashi don ya duba dokinsa, amma dokin ya shure shi a kan cibiya da dare ya fadi matacce. Da aka ba wazirinsa labarin abin da ya faru, sai nan da nan shi ma ya hau dokinsa, dokin ya ka da shi wuyansa ya karye, ya mutu. A cikin daren nan kuma manya-manyan sarakunansu bakwai suka ce ga garinku. Sai niyyar Kwararrafawa ta yaki ta wargaje, suka bar wajen. Daga nan Sarkin Katsina da kansa ya tafi wajen Danmasani ya durkusa ya yi masa godiya tare da goma na arziki.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "‘‘Da duniya da gasƙiya, da",
"a": "ba a bar mazari tsirara ba",
"b": "ba a ɗaure ɗan sane ba",
"c": "ba a bar huntu a kasuwa ba",
"d": "an bar zama da ƙazama.",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "Wane mataki aka ɗauka a kan arnan nan?",
"a": "Tura masu soja",
"b": "Rarrashin su",
"c": "Zarzagin su",
"d": "Janye masu soja",
"answerKey": "a",
"context": "“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe, ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Juji[Maryam Sa16]",
"a": "Shara",
"b": "Gwata",
"c": "Kwata",
"d": "Kazanta",
"answerKey": "a",
"context": "Kudan gida na daya daga cikin abokan gabarmu. manya masu raba cuta ga 'ya Adam. Shi ke kawo su, atuni', da ciwon gudawa da sauran irinsu.\n Amma shi kuda ba ya cizon mu kamar sauro da Isando. Hanyar da ya ke bi ya yi nasa mugun aiki ba daya ba ce da tasu. Su, suna tsotso kwayoyin cuta daga Cikin jini ne, su je su soki mai lafiya su dura masa. Amma bakin kuda ba a yi shi don ya yi cizo ba. Kuda ba ya iya huda fatar mutum, ba ya ma iya huda fatar kome, ko yana so. Harshensa da bakinsa duka taushi\ngare su.\nTsaya ka ji kazantar kuda. Ka san lalle, ko ba don cuta ba, kuda abin kyama ne. Wajibi ne kuma mu yi iyakar kokarinmu mu rabu da shi.\nBa abin da kuda ke so kamar ya ci luroson (najasar) dan Adam. In ya samu najasa, ya duka da ci, sai ka ce ka samu taliya. Kun san kuwa, in mutum ba shi da lafiya sau da yawa akan sami kwayoyin cuta a cikin najarsa.\nKai duk dai wurin kazanta, Mahauta ne, juji ne, wurin mushe ne, wurin gyambo ne duka dai nan ne fadar kuda.\n In sun ci sun taso, sai su yi face-face da kazantar har da kwayoyin cutar da ke ciki.\nDa ma kafafuwansu da ikinsu gashi gare Su, duk kuwa madauka dauda ne.\n \nDaga nan sai su zo su sauka kan abincinmu. \nKan san galibi, abincinmu wanda suka fi so shi ne kilishi, tsire, nono, sukari da su alewa. Kaga wadannan, in an saya ba a sake dafa su. saboda haka muna cin kazanta da yawa daga gare su.\n Ban da wannan ma, in suna cin abincinmu, sukan rika amai bisansa suna tashi. Kazanta bisa kazanta! Ina ka ga lafiya?\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Wane rukunin waƙoƙin mata aka fi sani da batsa da zage-zage?",
"a": "Na daɓe",
"b": "Na raino",
"c": "Na talla",
"d": "Na daka",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "Farauta da tsuntsaye ta shahara a kasashen",
"a": "Farisa, Hindu da Turai.",
"b": "Hindu, Faranshi, Turai da Nijer.",
"c": "Nijeriya, Faranshi, Hindu.",
"d": "Ingila, Hindu da Turai.",
"answerKey": "a",
"context": "Tsuntsaye wadanda ke farautar nama suna da halitta daidai wadda za ta dace da wannan aiki. Ga baki mai[Maryam Sa25] karfi da kaifi ya lankwasa kamar kugiya. Da shi suke kekketa nama. Ga su da kafa mai karfi da kumba zako-zako. In sun kawo sura, da su su ke fyauce[Maryam Sa26] abin da suka farauta, su rike, su yi sama da shi. In za su ci, sai su kakkafa kumbobinsu ciki, su rike shi kam.\n Shaho yana da saurin tafiya. Akwai wasu iri, in sun ga wani tsuntsu yana tashi sai su bi, kome saurin tashinsa, sai sun ishe sun buge. Su irin wadannan, mutane sun dade suna kiwon su domin farauta. In za a farauta, sai ka dauki shahonka a kafada, an daure shi da sarka, an yi masa lullubi. In ka ga ko hasbiya tana tashi, sai ka bude kan shahonka ka sake shi, ya buge\nmaka.\nWannan irin farauta ta shahara a kasashen su Farisa da Hindu. Da, hara Turai an yi, amma yanzu an daina.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Hula habar kada, na nufin",
"a": "hula mai kunne.",
"b": "hula zanna.",
"c": "doguwar dara.",
"d": "hula zita.",
"answerKey": "a",
"context": "Yau Jumma'a Malam Nomau za shi cin kasuwa Wudil. Kafin ya tafi ya dauki wandonsa mai kamun kafa, ya bude ya sa shi ya zuba babbar rigarsa bullan da hular dara da falmaran, da takalmi sani tsalle, da 'yar ciki, da rawani mubarashi ya rataye shi. Kuma yana saye da wando buje da 'yar shara, da hula habar kada da takalmin fade.\nDa isowarsa kofar gari sai ya raba gindin wata tsamiya ya fito da kayan nan nasa na cikin wando ya caba ado bayan ya wanke jikinsa. Ya kuma zuba turare dan-goma, ya bara goro marsa ya cika bakinsa ya yi kumurya. Ya kunshe tsofaffin kayansa buje, ya make a hammatarsa ya shiga gari ya kai gidan abokinsa ya ajiye. Matar abokinsa ta ba shi farau-farau ya sha. Daga nan sai ya tafi cin kasuwa.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Wane ne ya aiki Gujalo zuwa Makka?\n",
"a": "Mai Dunama",
"b": "Ukba ibn Nafi",
"c": "Mu'awiyya",
"d": "Halifa Abubakar",
"answerKey": "a",
"context": "\nShigowar Musulunci Kasar Hausa\n Masu ilmin tarihi sun nuna cewa kafin Musulunci ya iso ƙasar Hausa sai da ya fara biyowa ta wasu sassa na ƙasashen Afirka ta Yamma tukuna. kamar Senegal da Mali, a wajen ƙarni na goma sha ɗaya. Amma kuma malaman addini kamar limamin Bauchi Alhaji Ahmadu Muhammad da Alhaji Nasiru Kabara na Kano sun nuna cewa Musulunci ya iso Afirka ta Yammna,musammart Agadas da Barno, sannan ya ƙaraso ƙasar Hausa tun a zamanin Sayyadina Mu'awiyya dan Safiyanu, wanda ya turo Uƙuba Ibn Nafi ya zo ya kawo Musulunci da litattafan addini Afrika ta Yamma. Shi dai Sayyadina Mu'awiyya ya yi zamani ne a ƙami\nIna 7.\n Waɗansu malaman kuma sun nuna cewa Musulunci ya shigo Barno a zamanin sarautar Mai Dunama (1098-1150) wanda ya aiki wakilinsa Gujalo zuwa Makka wajen Halifa Abubakar Sadik (632-634) don ya karɓo saɗon Musulunci. Amma Gujalo ya tarar Halifa Abubakar ba shi da lafiya, har ma ya yi wafati, Gujalo bai sami saduwa da shi ba. Sai Sayyadina Umar ya hau Halifa (634-644), ya sadu da Gujalo, ya haɗa shí da manzonsa Amr bn Asi, ya ba shi Kur'ani mai girma da rawunna, da takobi, da garkuwoyi, da masu, da alkyabba iri-iri, da 'yan rakiya Larabawa ɗaruruwa don a kai wa Sarkin Barno. Da suka isa Barno sai suka shiga yaɗa addinin Musulunci da koyar da ilmi. Daga cikin Larabawan da suka biyo Gujalo, kimanin 300 suka bazu cikin kasar Hausa suka yaɗa Musulunci da koyar da ilmi.",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "‘‘Balarabe na Balaraba Sannu Balaraba Sai wata rana.’’ Me Haruna Uji, ke nuna wa a wannan tsakure?",
"a": "Dangantakarsa da Balaraba",
"b": "Ambaton Balaraba",
"c": "Ban kwana da duniya",
"d": "Yabon Balaraba",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "Mece ce dangantakar Gizo da Ƙoƙi a tatsuniyoyin Hausa?",
"a": "Miji da mata.",
"b": "Ubangida da baranya.",
"c": "Uba da ‘ya.",
"d": "Wa da ƙanwa.",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "Wacce ke da hanyar jam’i daban?",
"a": "Kwabri",
"b": "Hula",
"c": "Rumbu",
"d": "Kwando",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "Daga cikin muhimman ayyukan waziri, akwai",
"a": "ba wa sarki shawara",
"b": "ɗaukar nauyin baƙi",
"c": "saukar da baƙi",
"d": "kula da gidan sarki",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Ana fitar da mataccen jini daga jiki ta hanyar",
"a": "ƙaho",
"b": "rauni",
"c": "sakiya",
"d": "tsaga",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Ci tura na nufin...\n",
"a": "faskara",
"b": "gudana",
"c": "juya",
"d": "yiwu",
"answerKey": "a",
"context": "“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe, ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Da Sarki ya gudu, ina ya nufa?",
"a": "Lafai[Maryam Sa11]",
"b": "Agaie.",
"c": "Kogin Kaduna.",
"d": "Egbaji.",
"answerKey": "a",
"context": "A shekara ta 1897 zamanin Sarkin Bida Abubakar, Turawa suka yi karon batta da Nufawa. Kafin nan, Turawa sun shekara uku cur suna godo da sarki su hadu da shi cikin aminci a wani wuri da ake kira Egbaji, yana kin zuwa. Har ma a wani lokaci sai da Turawan suka nada wani Muhammadu Makun a madadinsa. Duk da haka a cikin 1900 kusan a ce sarki biyu ke akwai a Bida, tsohon sarki da wanda Turawa suka nada.\n Ana cikin haka, ran nan dai sai Gwamna Lugga ya aika wa Sarkin Bida da takarda, ya ce masa ya dai yi kokari ya zo ya sadu da shi a fadar Kogin Kaduna, kuma kada ya ii tsoron kome. Gwamna ya kara da cewa ba abin da za a yi masa, zai zo lafiya ya koma\nlafiya.\n A wannan karon ma sai Sarkin Bida ya ki zuwa. Makun ne da 'yan rakiyarsa suka amsa kira, suka je wurin Gwamna Lugga. Saboda haka Turawa suka dauri aniyar zuwa Bida. Suka shaida wa jama'a muddin dai ba an taba su ba, babu fada. Kuma duk mutumin da suka ga don ganin su ya yi haramar gudu, za su dauke shi a mazaunin makiyinsu. Har ma Gwamna Lugga ya aika wa Sarki Abubakar da cewa kodayake dai Makun ne suka dauka kamar sarki, duk da haka idan shi\nAbubakar ya yarda suka sadu ko a Bida ne, ba zai wulakanta shi ba. Zai sa shi cikin jin dadi har abada.\nAmma duk a banza. Maimnakon ya tauso sai ya gudu ya tasar wa Lafai. Amma fa fitar kutsu ya yi, domin daga shi sai fadawa kamar shida ya bar Bida Aka yi irin abin nan wuji-wuji-ina-gabas, aka i xashe[Maryam Sa8] manyan sarakunansa, aka yi wa wadansu iaur[Maryam Sa9] , aka kama na kamawa. Wadanda aka kama bayan sun wartsake sarai aka sake su. ",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "A lafazin kalma, wane wasali ke ganɗanta |g|?",
"a": "/a/",
"b": "/u/",
"c": "/o/",
"d": "/e/",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "Marubucin ya kwatanta bauna da barewa domin kawai tana",
"a": "iya tsalle da gudu.",
"b": "kwana a daji.",
"c": "iya cin ciyawa.",
"d": "da zane mai kyau",
"answerKey": "a",
"context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18] maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Idan aka kira mutum inuwar giginya ana nufin ba ya kyautata wa",
"a": "makusantansa",
"b": "kansa",
"c": "magabatansa",
"d": "kowa",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "Wane ne tauraron labarin ‘Kwaɗayi Mabuɗin Wahala…’ na Magana Jari Ce Na III na A. Imam ?",
"a": "Ɗandamau",
"b": "Sarkin Fawa",
"c": "Sarkin Fada",
"d": "Nababan – Jaji",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Literature"
},
{
"question": "Wanne ne gaskiya dangane da makaɗan fada?",
"a": "Sarkinsu na sa su yi wa wani waƙa.",
"b": "Ba su karɓar kyauta sai daga sarki.",
"c": "Ba su yi wa kowa waƙa sai sarki.",
"d": "Dukkansu makaɗan taushi ne.",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
},
{
"question": "A labarin, kalmar ƙware na daidai da",
"a": "gwanance",
"b": "saba",
"c": "dace",
"d": "haɗu",
"answerKey": "a",
"context": "A karkara da ma wasu manyan garuruwa ƙalilan, mutane kan haɗu su riƙa cin abinci tare. Akan zaɓi gidan mutum ɗaya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zaɓi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala sosai zuwa gidan, musamman da damina.\n\nA wurin haɗuwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka ƙware suke shan yabo da godiya. Waɗanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. Saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al’amari ya yi muni ke nan.\n\nCikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da ɗan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin waɗannan nau’o’in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganta da irin cefanen da maigida ya yi. Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. Wanda ma ba ya da ƙarfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Mece ce dangantakar Salihi da Ɗahira?",
"a": "Ɗa da Uwa.",
"b": "Uba da ‘ya.",
"c": "Miji da mata.",
"d": "Wa da ƙanwa.",
"answerKey": "a",
"context": "A wani gari can yamma da Magumi, wai shi Tsauni, an yi wani yaro mai suna Salihi. Iyayensa ba masu wadata ba ne, amma sun yi ƙoƙarin ganin ya yi ilmin boko da na Arabiya. Bayan Salihi ya kammala karatun firamare, sai mahaifinsa Tanimu, ya nema masa makarantar gaba da firamare. Domin an ce ‘‘Ilimi gishirin zaman duniya.’’ Amma kuma samo wa Salihi babbar makarantar Magumi bai yi wa mahaifiyarsa Ɗahira daɗi ba, don ba ta son ɗanta ya yi nesa da ita. Dalili shi ne ɗansu tilo namiji, sauran huɗun kuwa duk mata ne. Bugu da ƙari, tana jin munanan labarai iri-iri da kan faru a irin waɗannan makarantu.\n\nBayan Salihi ya isa makaranta, sai ya duƙufa kan karatu gadan-gadan. Zuwansa ke da wuya, sai suka ƙulla abota da wani ɗan ajinsu, wai shi Kasa. Kafin ya ankara, sai da abokinsa ya jefa shi cikin wata ƙungiyar asiri.\n\nDa ya farga da halin da ya shiga, sai ya yi ƙoƙarin fita daga cikinta, amma aka nuna masa ai ba a haka. ‘‘ In har ka ce za ka fice, lallai za a kassara ka, ko ma a halaka ka’’ in ji abokinsa.\n\nGanin halin tsaka-mai-wuya da ya shiga, sai ya tsayar da shawarar ya fallasa ƙungiyar, in ya so komai ta tafasa ta ƙone. Ya je ya shaida wa shugaban makaranta. Nan take ya sanya jami’an tsaro suka kamo dukkan ‘yan ƙungiyar. Kotu ta yanke musu hukunci, sannan aka kai su gidan jarun. Da ma an ce, ‘‘ Komai nisan jifa ƙasa za ya faɗo.’’",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Ana danganta itaciyar tsamiya da",
"a": "ƙwanƙwamai",
"b": "gajimare",
"c": "’yan ruwa",
"d": "dodanni",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Wanne ne keɓaɓɓen bayanin wasalin /a/?",
"a": "Ɗan tsakatsaki ne na ƙasa.",
"b": "Ɗan gaba ne na tsakiya.",
"c": "Ɗan ƙurya ne na sama.",
"d": "Ɗan gaba ne na sama",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
}
]